Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kimanin mutane miliyan 18 a yankin Sahel na fuskantar matsalar karancin abinci, a dai dai lokacin da wanda aka bayar a matsayin tallafi ke shirin karewa, gami da fuskantar karancin kudaden dorewar shirin tallafin.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce rikice-rikice, da annobar COVID-19, da sauyin yanayi da kuma hauhawar farashin kayayyaki ne ke kara jefa miliyoyin mutane a yankin kudu da Saharar Afirka cikin halin kaka ni kayi.
WFP ta ce tuni ta rage adadin tallafin abinci a wasu yankunan da abin ya shafa, yayin da ake fuskantar raguwar himmar masu bayar da agaji na kasa da kasa.
A farkon watan Afrilu, kungiyoyin bada agaji na duniya suka yi alkawarin taimakawa kasashen Sahel da wadanda ke kewaye da Tafkin Chadi da kudin da ya kai kusan Dala biliyan 2 domin shawo kan yunwar da ta addabi yankunan biyu.
Kasashen da ake saran su ci gajiyar taimakon sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Najeriya wadanda tashe tashen hankula da kuma karancin ruwan sama suka hana aikin noma da samar da abinci.
A wani labari na daban Cibiyar da ke da kula da abinci ta nahiyar Afrika ta ce matsalar karancin abinci na ci gaba da girmama a yankin Sahel, da kasashen yankin yammacin Afrika, inda yanzu haka kimanin mutane miliyan 23 da dubu 700 kwatankwacin kashi 7.4 na al’ummar kasashe 15 da aka nazarta ke cikin matsalar.
Wannan adadi dai na iya karuwa a wannan lokaci na tsakanin rani da damina kamar yadda alkaluman cibiyar suka nuna cikin wani rahoton karshen shekara da ta fitar.
Kimanin mutane miliyan 33 da dubu dari 4 ne za su iya fadawa cikin matsananciyar barazanar karancin abinci idan har ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba, a cewar wata kwararriya daga cibiyar wadda ke taronta ta hoton bidiyo.
Jami’ar ta ce adadin na wakiltar kashi 10.5 na al’ummomin kasashen.
Laurent Bossard babban daraktan cibiyar hadakar kasashen sahel da na yammacin afrika (CSAO), ya ce babban dalilin faruwar matsalar karancin abincin ita ce, rashin tsaro da tashe tashen hankulla da yankin ke fama da shi
Inda ake da fagagen daga guda 2 daya na cikin yankin da ya hada iyakokin 3 da suka hada kasshen Mali, Burkina Faso da Niger, inda ake kai munanna hare haren ta’addanci dake haifar da hasarar rayuka masu yawa daga mayakan kungiyoyin yan ta’addan Al-Qaïda (ISIS).
Fagen daga na biyu kuma shi ne wanda ya hada yankunan kasashen yankin tafkin Tchadi Najeriya Nijer Tchadi da kuma Kamaru, yankin da ya kasance maboyar kungiyar Boko Haram da ballalinta, da kuma kumgiyar Iswap dake biyayya ga kungiyar ISIS.