Yau Asabar bikin ranar Kirsimeti ya kankama a tsakanin miliyoyin mutane musamman mabiya addinin Kirista a sassan duniya.
Sai dai bikin wannan rana ya zo ne, a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Korona na Omicron ke ci gaba da yaduwa, lamarin da ake ganin zai rage armashin bikin a bana, kamar yadda annobar at Korona ta yi a shekarar bara, abinda ya sa mutane da dama da za su gudanar da bikin na Kirsimati killace a gidansu.
A can Bethlehem wurin da mabiya addinin Kirista suka yi amanna cewa, nan ne mahaifar Annabi Isa Alaihi-s-salatu wassalam, masu gidajen otel-otel sun shiga damuwa saboda karancin baki da cutar ta Korona ta takaita adadinsu a bana, yayin da kuma Isra’ila ta rufe kan iyakokinta.
Bayanai sun ce cikin daren ranar Juma’a, wato jajibirin ranar bikin Kirisimeti, tsirarun mutane ne suka gudanar da taron addu’a a birnin na Bethlehem, al’amarin da ba a saba ganin haka ba.
Gwamnatocin kasashen Turai sun kafa wasu tsauraran ka’idojin yaki da cutar ta Korona, lamarin da ya rage wa bikin na Kirsimeti armashi.
Kasashe irinsu Netherlands da Spain da Italiya duk sun wajabta sanya takunkumin rufe baki da hanci musamman a bainar jama’a da zummar takaita yaduwar annobar a lokacin bikin na Kirsimati.
A wani labarin na daban Yau 25 ga watan Disemba mabiya addinin Kirista a sassan duniya ke gudanar da bikin Kirsimeti domin murnar tunawa da haihuwar Yesu da suke bautawa.
A jawabinsa a jajibirin Kirsemeti Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Francis ya bukaci mabiya su rungumi rayuwa mai sauki, ba ta neman mallakar abin duniya ba.
Idan an jima a yau Juma’a Fafaroma zai gabatar da jawabin sakonsa na Kirismeti ga dimbin mabiya darikar katolika a filin st Peters a fadar Vatican.
Ana sa ran Fafaroma ya yi kira ga sasantawa da juna musamman a kasashen da ke fama da rikici.