Karim Khan na Biritaniya ya kama aiki a matsayin sabon mai shigar da kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC inda ake sa ran zai fara ne da manyan kararrakin da ke gaban kotun, ciki kuwa har da batun zaluncin da ke wakana wanda Isra’ila take a kan Falasdinawa.
Sabon mai shigar da karar mai shekaru 51, ya maye gurbin Fatou Bensouda ta Gambiya, wacce ta fadada tsare-tsaren kotun ta ICC a tsawon shekaru tara da ta yi tana jagoranci, ciki har da wanke tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo.
Khan ya sha alwashin farfado da martabar kotun da ke dauke da dimbin manyan korafe-korafe a gabanta, duk da nasarorin da ta samu a baya.
Khan a baya ya jagoranci wani bincike na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan aikata laifuka daga kungiyar masu da’awar jihadi a kotun ta ICC.
Ana ganin tsohuwar mai shigar da karar kotun wato Bensouda ta bar shi da ayyuka masu zafi ciki kuwa har da batun bincike kan yadda ake yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar Philippines.
Baya ga wannan, akwai binciken da ake yi wa Amurka da aikata laifukan yaki a Afghanistan, sai kuma rikicin da ke wakana tsakanin Isra’ila da Falasɗinu.
Lauyan na Burtaniya zai kuma kalubalanci adawar manyan kasashe da suka ki shiga kotun ta ICC, irinsu Amurka da Isra’ila da China da kuma Rasha.
Babban lamarin da sabon mai shigar da karar yake fuskanta shine batun zaluncin da haramtacciyar kasar isra’ila take gudanarwa a kan larabawa falasdinawa.
Ana sa ran kotun hukunta manyan laifukan ta duniya ta dauki tsatstsauran mataki wanda zai kawo karshen bala’in da yahudawan sahayoniya ‘yan share wuri zauna, mazauna haramtacciyar kasar isra’ila suka sanya falasdinawan a ciki.