A ’yan kwanakin nan, majalissar wakilan Amurka ta kafa wani kwamiti da ta ce zai lura da batutuwa masu nasaba da takarar da kasar ke yi da kasar Sin, har ma majalissar na ganin kwamitin zai iya zama wata garkuwa da sabon abun da ya kira hanyoyi mabanbanta da Sin ke zama barazana ga Amurka.
Duk da cewa aikin da aka dorawa sabon kwamitin bai wuce na bincike da kuma ba da shawara ba, kafa shi wata manuniya ce ga kudurin siyasar Amurka, na nacewa tunanin cacar baka tsakanin ta da Sin.
Masharhanta da dama na ganin an kafa kwamitin ne domin karfafa matakan gwamnatin Amurka mai ci na dakile kasar Sin, karkashin amincewar majalissar dokokin kasar, da goyon bayan gwamnatin shugaba Joe Biden, wanda ko shakka babu cikin tsawon lokaci, tasirin hakan zai ci gaba da illata alakar Sin da Amurka.
Idan mun waiwayi tarihi, za mu ga bayan aukuwar harin 11 ga watan Satumban 2001, Amurka ta mayar da batun yaki da ta’addanci sahun gaba, a manufofinta na tsaro da diflomasiyyar kasashen waje.
Daga bisani kuma a shekarar 2017, gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta bullo da abun da ta kira matakan tsaron kasa, wanda karkashin hakan ta ayyana kasar Sin a matsayin “Muhimmiyar abokiyar takara” ga Amurka.
Tun daga wannan lokacin ne kuma, Amurka ke ci gaba da bunkasa wannan manufa ta fuskoki daban daban.
To sai dai abun tambaya a nan shi ne, tun daga waccan manufa ta tsaron kasa, wadda karkashinta Amurka ta rika yakar kasashe daban daban, tare da haifar da mummunan tasirin yaki kan miliyoyin fararen hula, har zuwa dokar ayyana Sin a matsayin barazana ga Amurka, wacce manufa ce a cikin su ta haifarwa Amurka wani alfanu?
Sanin kowa ne cewa, manufar Amurka ta yake-yake, da daura damarar yin takara maras adalci, ko rarraba kan yankunan duniya zuwa rukunoni, da maida wasu sassa saniyar ware, ba abun da suka haifarwa kasar sai koma baya, da kara jefa al’ummun duniya cikin mummunan yanayi.
Don haka dai ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta yi watsi da manufofin wariya da nuna kyama, ko yunkurin dakile kasar Sin ta dukkanin fannoni, kafin hakan ya kai ga haifar da mummunan sakamako da zai jefa Amurka cikin halin matsin tattalin arziki, tare da gurgunta alaka da moriyar sassan biyu.
Source:LegitHausa