Sabon Fira Ministan Somaliya Ya Karbi Ragamar Jagorancin Kasar A Hukumance.
Sabon fira ministan Somaliya Hamza Abdi Barri ya karbi ragamar jagorancin kasar a hukumance.
Rahotonni sun bayyana cewa: Sabon fira ministan Somaliya Hamza Abdi Barri ya karbi ragamar jagoranci kasar a hukumance daga hannun tsohon fira ministan kasar Muhammad Husain Roble a sabuwar hedkwatar gwamnatin tarayyar kasar da ke birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a jiya Talata.
Tsoffin ‘yan Majalisun ministocin Somaliya da jami’an gwamnatin tarayyar kasar gami da babban bako a wajen bikin mika ragamar jagorancin kasar wato jakadan kasar Qatar a Somaliya Hasan bin Hamza Hashim duk sun halarci zaman taron.
READ MORE : Bulgariya Ta Kori Jami’an Diflomasiyyar Rasha Guda 70 Daga Kasarta.
Tun a ranar Asabar din makon da ya gabata ce Majalisar Dokokin Somaliya ta kada kuri’ar amincewa da Hamza Abdi Barri a matsayin sabon fira ministan kasar, bayan da shugaban kasar ta Somaliya Hasan Sheikh Mahmud ya nada shi a ranar 15 ga wannan wata na Yuni.
READ MORE : Masar Ta Karyata Batun Cewa; Tana Hana ‘Yan Sudan Shiga Kasarta.
READ MORE : Kasar Iran Ce Kan Gaba A Fagen Yaki Da Muggan Kwayoyi A Duniya.
READ MORE : Sojojin Amurka da na Birtaniya sun shiga tashar ruwan Nastoun na kasar Yamen.