Sabbin luguden wutar da Isra’ila ta kwashe kwana 77 tana yi a Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 20,000, da jikkata fiye da 52,600.
Munir Al Bursh, babban daraktan Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ya samu rauni, kuma an kashe ‘yarsa. / Photo: Reuters
1358 GMT — Sabbin hare-haren Isra’ila sun kashe gomman mutane ‘yan gida daya a Gaza
An kashe da raunata mutane da dama ‘yan gida ɗaya a wasu hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a ranakun Alhamis da Juma’a, a kan gidajensu a garin Jabalia da ke arewacin Gaza.
Munir Al Bursh, babban daraktan Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ya samu rauni, kuma an kashe ‘yarsa.
Bugu da kari, wasu daga cikin iyalansa na Al Bursh da kuma dangin ɗan’uwansa sun sami raunuka sakamakon wani harin da Isra’ila ta kai kan gidan ɗan’uwansa da ke Jabalia a yammacin ranar Alhamis.
A wani harin da aka kai ta sama, majiyoyin likitocin Falasdinawa sun shaida wa wakilin Anadolu cewa an kashe Falasdinawa 16, sannan wasu kusan 50 suka jikkata, kuma dukkansu ‘yan gidan Al Bursh ne.
Wannan ya faru ne sakamakon harin da aka kai ta sama da aka kai a gidan iyali a Jabalia.
1055 GMT — An juya akalar jiragen ruwa 170, an kuma tsayar da 35 saboda hare-haren Houthi a Bahar Maliya
A cewar wata sanarwa da kamfanin da ke San Francisco ya fitar, kimanin jiragen ruwa 170 masu ɗauke da kwantena aka mayar da su zuwa kasashen Afirka.
Kamfanin jigilar kayayyaki na Amurka Flexport Inc ya ce an karkatar da jiragen ruwa kusan 170 daga Mashigin Bab el Mandeb da ke Bahar Maliya kuma an dakatar da jiragen ruwa 35, suna jiran umarni daga kamfanonin da suke yi wa aiki.
A cewar wata sanarwa da kamfanin da ke San Francisco ya fitar, kimanin jiragen ruwa 170 masu ɗauke da kwantena aka mayar da su zuwa kasashen Afirka, yayin da wasu jiragen ruwa 35 suka tsaya cik sakamakon hare-haren da aka kai a Tekun Bahar Maliya.
A gefe guda kuma, kungiyar Houthi a Yaman ta ci gaba da yin barazanar kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaka da Isra’ila da ke ratsa mashigar tekun da ke kudu da Tekun Bahar Maliya, don goyon bayan Falasdinawan da ake ta yi wa ruwan bama-bamai a Gaza.
Source: TRTHausa