Sabbin hanyoyi biyu masu sauki na rage matsananciyar ƙiba daga Ingila da Amurka.
Nan ba daɗewa ba mutanen da ke fama da narkekiyar ƙiba za su samu sauƙi saboda za a samar da wata allura da za su dinga yi duk sati da za ta taimaka musu wajen rage kitse.
Allurar ta semaglutide na kamfanin Wegovy, kan sa mutum ya ji shi a ƙoshe ta yadda ba zai dinga buƙatar cin abinci sosai ba kuma ba zai dinga jin yunwa sosai ba.
A yayin gwajin samar da allurar, wanda aka haɗa shi da cin abinci mai kyau da motsa jiki, ya taimaka wa mutane masu matuƙar ƙiba su rage kashi 10 cikin 100 na ƙibarsu.
Kuma Cibiyar Lafiya ta kasa a Ingila wato National Institute for Health and Care Excellence NICE, ta bayar da shawarar cewa ya kamata a sanya allurar a tsarin hukumar lafiya ta Birtaniya NHS.
Sai dai har yanzu ba a kai ga amincewa da shawarwarin da NICE ta gabatar a Ingila da Wales ba, har sai an bi waɗannan ƙa’idojin:
- ya kasance ƙwararren likita ne ya ba da izinin a yi ta
- ya kasance an rubuta ta ne ga masu matsananciyar ƙiba da ke jawo musu matsalar hawan jini ko ciwon zuciya
- ya kasance an yi ta ne na tsawon shekara biyu kawai
Mutum zai yi wa kansa allurar ne.
Yana da kyau mutane masu matsananciyar ƙiba su dinga tuntuɓar likitocinsu a kan batun rage ƙiba ba tare da wata illa ba.
Wasu kuma suna rage ƙiba ne ta hanyar kula da irin abincin da ya kamata su ci da kuma motsa jiki.
- Abin da ya sa mata suka fi fuskantar haɗarin mutuwa idan likitoci maza suka yi musu tiyata
- Sarƙaƙiya uku da ke tattare da yi wa mutum dashen zuciyar alade
Wata sabuwar hanyar rage ƙibar daga Amurka
Masana kimiyya a Amurka sun ce kara sa’o’in baccin ka da sa’a guda da kwata a kowanne dare na iya taimaka maka wajen kona kitsen calories 270 a rana guda.
Tawagar masana daga cibiyar bincike kan bacci da ke Jami’ar Chicago ta ce kwanciya da wuri na taimaka wa wajen rage kwaɗayi da ciye-ciyen dare, kuma sannan samun hutu sosai na rage kwaɗayi.
Binciken ya yi nazari kan mutum 80 da suka haɗa da maza 41 da mata 39 waɗanda dukkansu mutane ne da ke fama da ƙiba, sannan sun ksance suna yin baccin ƙasa da sa’a shida rabi a kowane dare, ƙasa da sa’a takwas da ake buƙatar mutum ya samu a kowane dare.
An ɗora wadannan mutane a kan starin ingantaccen bacci ta hanyar tattaunawa da su da shawarwari domin ƙara sa’o’in barcinsu.
An yi amfani da wannan tsarin wajen gwada sauyin da ke tafiya da jikinsu da lissafin adadin kitsen da suke ƙonewa a kowane dare.
Farfesa Esra Tasali da ta jagoranci binciken ta ce samun wadataccen bacci na kawo sauyi a rayuwa, musamman ga mutanen da ke fama da matsalar ƙiba.
“Wannan bincike ya kawo ƙarshen nazarin da aka kwashe sama da shekara 15 ana yi a kan alaƙar barci da ƙiba da kuma kuzari.
“Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ɓata bacci ko rage yawan bacci na da alaƙa da na’urorin zamani ko wayoyi da galibin mutane ba sa iya rayuwa sai da su, ko kuma baa lokaci wajen amfani da su kafin kwanciya bacci
Sauran hanyoyin rage ƙiba sun haɗa da:
- orlistat – wata ƙwayar magani da ke hana kitse cikin abinci shiga cikin jiki
- liraglutide, na kamfanin Saxenda – wata allura da ake yi kullum-kullum da ke sa mutane su ji su a ƙoshe ko ba sa jin yunwa
- wani abu da ake ɗaurawa a kan ciki da zai sa mutum ya ji shi a ƙoshe
- wata tiyata da ake yi ta gastric bypass or bariatric surgery
Kusan mutum ɗaya cikin huɗu ne ke fama da matsananciyar ƙiba a Birtaniya kuma hajkan yana sa su fuskantar barazanar kamuwa da wasu cututtuka.
A shekarar 2018 zuwa 2019, mutum 11,117 aka kwantar a asibiti a Ingila saboda matsananciyar ƙibarsu.
Helen Knight ta Cibiyar Lafiya ta Ingila ta ce: “Mun san cewa matsananciyar kiba na ɗaya daga cikin matsalolin da muke fuskanta a fannin lafiya.
“Matsalar lafiya ce da ke buƙatar likitoci su shiga ciki, saboda tana taɓa lafiyar hankali da na tunani.”