Sabanin Siyasa A Kasar Libya Yana Ci Gaba Da Yin Tasiri A Yawan Man Fetur Din Da Kasar Take Fitarwa A kowace Rana.
Dambaruwar siyasar kasar ta Libya dangane da ci gaba da zaman Pira minista Abdulhamid Dubaibah akan mukaminsa, ya haddasa raguwar man fetur din da kasar take hakowa zuwa ganga 800,000.
Gabanin juma’ar da ta gabata kasar ta Libya tana fitar da man fetur da ya kai ganga miliyan daya da dubu dari uku a kowace rana.
An rufe daya daga cikin manyan cibiyoyin hako man fetur na kasar wanda ake kira da “ al-shararah” a yammacin kasar da yake samar da ganga 300,000 a kowace rana. Hakan dai ya biyo bayan gangamin da wasu mutane su ka yi a bakin cibiyar domin yin kira ga Dubaibah da ya sauka daga kan mukamin nasa.
Wata cibiyar hakar man fetur din da ta tsaya da aiki, ita ce ta “ FIl” da take iya fitar da gangan 65,000 a kowace rana.
READ MORE : Iran Tana Son Bunkasa Alakarta Da Kasashen Nahiyar Africa.
Bugu da kari, wasu masu Zanga-zangar sun hana motocin daukar man fetur motsawa a tashar jirgin ruwa ta “al-Buraiqah” a jiya Talata.
READ MORE : Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan IPOB a Imo.