Shugaban Rwanda Paul Kagame ya ce, nan gaba kadan kasar za ta fadada yarjejeniyar karbar bakin-haure mai cike da sarkakiya da ta kulla da Birtaniya saboda yadda tsarin bada mafakar ya gurgunce.
Kagame wanda zai jagoranci taron kungiyar kasashen rainon Ingila a makon da muke ciki karo na 54, ya ce ya amince yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki, duk da tutsun da yake fuskanta daga kungiyar kare hakkin dan adam ta kungiyar tarayyar Turai.
Tun da fari dai, Birtaniya ta shirya tsaf ne don mayar da bakin-haure da kuma masu neman mafaka zuwa Rwanda ta cikin wata sanarwa da tuni Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da ita.
A farkon watan nan ne dai aka shirya jirgin farko na masu neman mafaka ya shirya tashi daga Birtaniya, sai dai kuma an dakatar da shi saboda umarnin kotun Tarayyar Turai na dakatar da shirin.
A cewar shugaban na rwanda, sama da shekaru 30 Rwanda ke rike da ‘yan gudun hijira sama da dubu 100 a don haka ba sabuwar matsala bace ga Rwanda.
Kagame ya kuma kara da cewa duk da tustsun da shirin ke fuskanta daga bangarori da dama, amma Rwanda za ta fadada shirin zuwa sauran kasashe.