Da safiyar ranar Lahadi ne dakarun Russia suka harba makami mak linzami zuwa birnin Kyiv na Ukraine, a wani mataki na ci gaba da mamayar kasar.
An jiyo karar ababen fashewa a sassa daban-daban na birnin Kyiv din.
Magajin birnin, Vitali Klitshko, ya ce tuni motocin daukar marasa lafiya hade da ma’aikatan ceto suka isa wurin.
Harin Russia na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sake kira ga aminan Ukraine su kai musu daukin makaman kare sararin samaniyar kasarsa.
A bidiyon da ya ke wallafa a kowanne dare tun bayan fara yakim, Mista Zelensky, ya ce yakin da suke yi da Rasha ya shiga wani mataki mai sosa rai da tsananin wuya, bayan Rasha ta karbe birnin Severodonetsk.
Yakin dai ya faro ne tun a watan Fabrairun 2022, wanda yanzu ya kawo sama da watanni 4 ke nan ana gwabzawa.
Yakin ya yi sanadin rasa rayukan dubban mutane daga tsagin Ukraine da Rasha, ciki har da manyan dakarun sojin kasashen biyu.
A wani labarin na daban Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar.
Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.
Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.
Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar Edo.
Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Mista Adamu ya ce akwai takaici irin yadda yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.
” Ban damu da abinda ke faruwa a wata jam’iyya ba, damuwa ta itace abinda ke faruwa a jam’iyyata.”
” Babu Shugaba nagari da ba zai damu ba idan ya rasa mamba ko da daya ne a jam’iyyarsa, ballantana ayi maganar mamba biyu, ko uku.”, in ji Adamu.
Sai dai Shugaban APCn yace suna kan tattauna hanyar da zasu dinke wannan baraka ta ficewa daga jam’iyyar, duk da ya ce ba wani sabon abu bane.