Rundunar sojin kare juyin juya halin musulunci ta Iran (IRGC) a bayyana nasarar da ta samu a kallafaffaen yakin da amurka da kakaba tsakanin Iran da Iraki a shekarar 1980 a matsayin wata nasara wacce ba wanda zai iya musantawa, kuma hakan wata amsa ce da take tattabatar da cewa rana na zuwa wacce za’a fatattaki amurka daga gabas ta tsakiya.
A wani jawabin tunawa da yakin wanda ake gudanarwa duk shekara, karo na arba’in da daya da rundunar ta IRGC ta fitar ya tabbatar dacewa yakin wanda aka shafe shekaru 8 anayi bazai yiwu a alakanta shi da tsohon shugaban Iraki saddam hussain kamar yadda kafafen yada labaran yammacin turai ke yayatawa ba.
IRGC ta bayyana yakin a matsayin wani yunkurin da amurka da kawayen ta sukayi domin kokarin rushe nizamin jamhuriyar musulunci na Iran wanda a lokacin bai jima da samun kafuwa a kasar Iran din ba.
IRGC ta bayyana cewa amurkan da kawayen ta sunyi wancan yunkuri ne domin gwada sa’ar su a karo na karshe domin dawo da tasirin su na kama karya a kasar ta jamhuriyar musulunci ta Iran wacce ta samu sauyi daga ikon sarki shah zuwa gwamnatin musulunci karkashin Ayatollah Khumaini.
A yayin allafaffen yakin wanda ya kwashe shekaru takwas anayi, wanda aka kallafawa jamhuriyar musulunci ta Iran din an take dukkan dokokin kasa da kasa inda akayiwa Iran din rufdugu amma dakarun na IRGC suka dake kuma suka tabbatarwa da duniya cewababu abinda zai sanya kasar ta kuma fadawa cikin tasirin amurkan da karnukan ta.
A lokacin yakin gwamnatin Iraqi ta wancan lokacin tana samun dukkan goyon baya daga amurka da kawayen ta a dai dai lokacin da aka hana Iran sayo makamai daga kasashen ketare.
A karshen jawabin rundunar sojin IRGC ta bayyana yadda amurka ta fice daga afghanistan a wulakance, hakanan kuma a bayyana bukatar korar amurka daga nahiyar asiya nan ba da jimawa ba.