Rukunin B na kunshe da kasashen Ingila da Iran da Amurka da kuma kasashen ko dai Wales ko Scotland ko kuma Ukraine, sai dai wadda ta yi nasara a karawar watan na Yuni tsakanin kasashen 3, saboda yadda aka dakatar da wasansu sakamakon rikicin Ukraine.
A rukunin C, akwai kasashen Argentina da Saudi Arabia da Mexico da kuma Poland.
Rukunin D na kunshe da kasashen Faransa mai rike da kambu da Denmark sai Tunisia, sai kuma daya daga cikin kasashen ko dai hadaddiyar daular larabawa ko Australia ko kuma Peru.
Rukunin E na kunshe da Spain da Jamus da Japan kana kasashen ko dai Costa Rica ko New Zealand
A rukunin F akwai kasashen Belgium da Canada da Morocco da kuma Croatia.
Sai rukunin G da ya kunshi Brazil da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru
Kana rukunin karshe na H da ke dauke da kasashen Portugal da Ghana da Uruguay da kuma Korea ta kudu.
A wani labarin na daban Sojin Mali ta ce ta kashe mayaka 203 a wani samame da ta kai a wasu yankunan kasar, lamarin da ke nuni da karuwar ba ta kashi tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyi masu ikirarin jihadi a kasar da yaki ya daidaita.
A cewar wata sanarwa daga rundunar sojin ta Mali, dakarun gwamnati sun kashe mayaka 203, suka kuma kama 51, tare da kwace dimbim makamai.
Sanarwar na zuwa ne bayan rahotannin da suka karade kafafen sadarwar zamani a wannan makon cewa an kashe gwamman mutane, ciki har da fararen hula a yankin Moura.
Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa ta ce har yanzu ba ta kai ga tantance sahihancin rahotannin biyu ba.