Wannan na zuwa ne a zaman da kungiyar ta gudanar yau a birnin Tehran tare da halartar wasu daga cikin mambobin kungiyar daga kasashe daban-daban, yayin da kuma wasu suka halarta ta hanayar hotunan bidiyo na yanar gizo, babban sakataren kungiyar Muhammad Ali Karimiyan ya bayyana cewa, wannan mataki da Amurka ta dauka na rufe shafukan na Iran yana a matsayin take hakkin fadar albarkacin baki.
Ya ce gwamnatin Amurka da sauran kasashen turai sun fi kowa babatu wajen ikirarin kare hakkokin jama’a na fadar albarkacin bakinsu, amma kuma abin da suke yi a kan wasu ya yi hannun riga da hakan, musamman idan lamarin ya shafi kasashe ko wasu bangarori ko kungiyoyi masu ‘yancin siyasa da neman ganin an yi adalci a cikin lamaurran siyasar duniya.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, irin gudunmawar da kafofin yada labarai na kasar Iran wadanda aka rufe da kuma na sauran bangarori masu ‘yancin siyasa suka bayar, wajen bayyana wa duniya zaluncin Isra’ila kan al’ummar falastinu, shi ne babban dalilin daukar wannan mataki.
Kungiyar hadin kan tashoshin rediyo da talabijin an kasashen musulmi tana mambobi daga kasashen duniya daban-daban, wadanda suka hadu kan cewa ba su amince da wannan mataki da gwamnatin Amurka ta dauka ba, na rufe wasu shafukan tashoshin talabijin na kasar Iran, da kuam wasu na yankin gabas ta tsakiya da ake adawa da salon siyasar danniya da mulkin mallaka na manyan kasashen duniya.
Ba yau ne ba dai kasar amurka ta fara daukan matakan da suka saba da dokokin kasa da kasa dangane da ‘yancin yada labarai da ayyukan jarida wanda hakan ke sanya aikin jarida da ‘yan jaridu cikin hadari gami da mayar musu da ayyuka baya.
Ana sa ran kungiyar hadin kan tashoshin radiyo da talbijin zasu dauki mataki kan wannan laifi da amurkan take aikatawa.