Tuni dai dangantakar Ronald Koeman da shugaban Barcelona Joan Laporta ta yi tsami a makwannin da suka gabata, kuma a bangaren sa Koeman ya ba da tabbacin cewar Laporta yayi kokarin lalubo wanda zai maye gurbinsa a watannin baya, amma yunkurin ya faskara, abinda ya sanya har yanzu akwai rade-radin kowane lokaci daga yanzu yana iya rasa matsayin sa.
Rashin nasarar da Barcelona ta kara yi a hannun Bayern Munich ya tabbatar da gibi mai fadi da ke tsakanin manyan kungiyoyin a nahiyar Turai, la’akari da lallasawar da Baryern ta yiwa Barcelonan da kwallaye 8-2, yayin wasan kwata final na gasar Zakarun Turan shekarar bara.
Koeman ya ce ba shakkah PSG ta yi musu wanka da ruwan sanyin da ke bayyana gaskiyar halin da suke ciki na matsalolin da suka tilasta musu fuskantar kalubale.
Dangane da batun makomarsa kuwa, Koeman ya kuma ce batun tunanin zai ajiye aiki ma bai taso ba, inda ya bayyana muhawarar da wasu ke yi kan batun a matsayin rashin hankali.
Yayin wasan na jiya Talata dai matashin dan wasan PSG Kylian Mbappe ya nuna kansa inda ya ci kwallaye 3, yayin da Moise Kean ya ci 1, a bangaren Barcelona kuwa Messi ne ya ci mata kwallon guda daga bugun fanereti.