Romania za ta karɓi ɗaliban Najeriya daga Ukraine su ƙarasa karatunsu a ƙasar.
Gwamnatin Romania ta yi tayin bai wa ɗaliban Najeriya damar ci gaba da karatu a jami’o’in ƙasar bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake tafkawa a ƙasar, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Najeriya.
Babban sakatare a ma’aikatar, Gabriel Aduda, ya ce ministan ilimi na Romania wadda maƙociyar Ukraine ce, shi ne ya bayyana hakan.
Mista Aduda ya ƙara da cewa yanzu haka suna tattaunawa da sauran maƙotan ƙasashe kamar Poland da Hungary da Girka don su bai wa ‘yan Najeriya irin wannan damar.
‘Yan Najeriya kusan 2,000 ne aka tabbatar sun tsallaka ƙasashe maƙotan Ukraine a yunƙurinsu na samun mafaka daga yaƙin da aka fara fafatawa ranar 24 ga watan Fabarairu.
Tuni aka kwaso ‘yan ƙasar kusan 1,000 amma har yanzu akwai ɗalibai a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnati don su koma gida.