Shugaban Ukraine Volodymr Zelensky ya gargadi cewa nan ba wasu sa’o’i kaɗan dakarun Rasha za su dirarwa birnin Kyiv a ƙoƙarin ƙwace ikonta.
A wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye zuwa ga ‘yan kasar, Mista Zelensky ya bukaci mutane su ci gaba da nuna jajircewa, yana mai sanar da cewa an riga an yanke hukunci kan makomar Ukraine.
Mazauna birnin Kyiv sun sake shafe wani dare a tashar jirgin kasa na karkashin kasa da duk wani wuri mai ginin karkashin kasa.
Sojojin Ukraine sun ce ana gwabza kazamin fada a yankin da sojojin Rasha ke kokarin sauka da jirginsu a nan birnin Kyiv din.
Sannan ana ci gaba gumurzu da Rashar a birane da dama na Ukraine, yayin da wannan yaƙi ke shiga kwana na Uku.
Rasha ta ce sojojinta sun shiga Melitopal da ke kusa da Crimea a kudu maso gabashi, duk da cewa babu tabbacin ikirarin nata zuwa yanzu.
Sai dai sojojin da ke kare Kharkiv da ke kusa da Iyakar a gabashi- na nuna jajircewa duk da yawan makaman roka da ruwan artillery da ake musu.
Kuri’ar MDD
Tuni dai Rasha ta yi watsi da daftarin Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna kin amincewa da mamayer ta a Ukraine.
India da China da Hadaddiyar daular Larabawa sun kauracewa zaman. Kasashe 11 mambobin majalisar sun nuna goyon-baya.
Jakadan Rasha, wanda shi ne shugaban kwamitin sulhu na Majalisar, ya dage kan cewa Rasha ba yaƙi take kaddamarwa kan Ukraine ba ko al’ummarta, sai dai kawai wannnan wani yunkurin ne na kare al’ummar Donbas.
Bayan kuri’a da aka kaɗa a Majalisar kan Rashar, Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta zargi Rasha da cin mutunci karfin ikonta.
Dubban ‘yan Ukraine na tserewa ta iyakoki domin shiga ƙasashe makwabta irinsu Poland da Romania, Hungary da Slovakia.
Ƙaƙaba Takunkumai
Fadar White House ta sanar da kakaba takunkumai kai tsaye kan Shugaba Vladmir Putin.
Wannan shi ne mataki na baya-bayanan a kokarin matsawa Moscow ta tsaigata wuta, takunkumai sun kuma hada da ministan harkokin wajenta Sergei Lavrov.
Matakin ya zo iri guda da wanda kasashen Turai da Burtaniya suka sanar kan kasar.
Wannan ba wai shi ne karon farko da kasashen yamma ke sanyawa shugaba a duniya mai karfi irin wannan takunkumi ba, amma ba kasafai aka fiye samu ba, musamman a lokuta irin wannan masu tunzuri – saboda Vladimir Putin shugaban kasa ne da karfin makamin nukilliya da kuma ke da kujera na dindindin a kwamitin tsaro na MDD.