An dawo da kashin karshe na ‘yan Nijeriya da suka makale a rikicin kasar Sudan, sun taso ne daga filin jirgin sama na Port Sudan.
Kawo yanzu gwamnatin tarayya ta dawo da ‘yan Nijeriya 2,518 gida.
Wannan rukunin sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a ranar Asabar, 13 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 6:36 na yamma a cikin jirgin kamfanin Tarco.
Jirgin dai ya kwaso ‘yan Nijeriya mutum 147 wanda wannan shi ne na biyu da kamfanin ya yi kan jigilar ‘yan Nijeriya. Jirgin na farko ya kwaso mutane 125.
An bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin guiwa a ranar Lahadi, wanda Amb. Janet Olisa, Daraktar Kula da Ofishin Babban Sakatare, Ma’aikatar Harkokin Waje (MFA) da Dr. Nasir Sani-Gwarzo, Babban Sakatare a Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Tarayya da Ci gaban Jama’a (FMHADMSD) suka fitar.
Dukkansu sun ce kwasu ‘yan Nijeriya daga Sudan yana daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa kada a bar wani dan Nijeriya da ke neman tsira daga rikicin kasar Sudan a baya.
A wani labarin na daban Rundunar ‘yansanda reshen jihar Ogun sun kama wasu ma’aikatan bankin bada lamuni (Micro Finance) har su hudu da laifin kashe wata matar kwastomansu ‘yar shekara 50 a lokacin da suke kokarin karbar lamuni da mijinta ya amsa.
Matar mai suna Vivian Omo, wanda ake zargin daya daga cikin ma’aikatan bankin ne mai suna Ajibulu, wanda shi ne yafi kaurin suna wajen sanadin rikicin mutuwar Matar bayan ya ture ta, sauran hudun: Badmus Olalekan, Ajibade Oludare, Eniola Aduragbemi da Femi Oloko an rahoto jami’an ‘yansanda sun cafke su baki daya a garin Ifo na jihar Ogun, inda lamarin ya faru.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, ma’aikatan bankin da ke da ofishi a garin Ifo a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, sun dira gidan kwastoman na su domin nemansa da ya biya bashin da ya karba, amma Matar ta shaida musu cewa Mijinta baya gida.
Amsar da Matar ta ba su sam ba ta yi wa ma’aikatan bankin dadi ba inda nan take suka fara tattara dukkanin kayayyakin alatu da ke gidan zuwa ofishinsu, amma marigayiyar ta hana su kwashe mata kaya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a lokacin da marigayiyar ke takaddama da ma’aikatan bankin, sai daya daga cikinsu mai suna Ajibulu ya tureta ta ke ta fadi a Sume aka garzaya da ita asibitin da ke kusa don ceto rayuwarta.
Amma Likitan da ke bakin aiki ya bayyana cewa “ta mutu”.