Hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana cewar rikicin hare haren masu ikrarin jihadi a yammacin Jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar kaurace war dumbin jama’a daga matsugunan su. Hukumar ta kuma jaddada cewar tsanantar kauracewar da jama’ar keyi ya fara ne a cikin watanni biyar na farkon shekara ta 2022 bisa zafafar rashin kwanciyar hankali da ake fuskanta da wasu ke kai hari ga fararen hula da jami’an tsaro ba kakkauta wa .
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana cewar an samu matsalolin tsaro har 136 daga watan Janairu zuwa Aprilun wannan shekara sabanin yadda ya kasance sau 93 a shekarar da ta gabata a dai dai irin wannan lokaci.
Rikicin ya haifar da daaga ranar daya 1 – 19 ga watan mayu an kashe fararen hula 43 tare da awun gaba da wasu 22 a sassan Torodi, Tera da kuma Gotheye a yankin Tillaberib dake da makobtaka da Burkina Faso da Mali a cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumar ta kara da cewa Tun daga farkon watan Afrilun wannan shekara da muke ciki ne dai fiye da mutane dubu 34,700 da ke zaune a Tillaberi matsalar rikicin ta tilasta musu ƙaura zuwa wasu wurare da zasu samu natsuwa.
Kasar ta Nijar na fama da matsalar hare haren masu ikrarin jihadi a kan iyakar kasar da Mali da Burkina faso ta yammaci da kuma gabar ta da Najeriya ta Kudanci
Kasar ta Nijar dai ta kasance matsuguni ga dubban wadanda suka kaurace wa matsugunan su tare da yan gudun hijra da suka tsere daga Najeriya, Mali da kuma Burkina Faso.