Wasu bayanai daga Chadi na nuna yadda mutane akalla 27 suka rasa rayukansu sanadiyyar wani rikicin da ya barke tsakanin Makiyaya da Manoma a gabashin kasar.
A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, ministan shari’a na Chadi Mahamat Ahmat Alhabo ya ce rikicin na da nasaba da badakalar da ta dabaibaye sayar da wasu filaye a kauyukan biyu.
A cewarsa, sarakunan gargajiyar kauyukan biyu sun sayar da filayen kiwo da na noma aba bisa ka’ida ba, matakin da ya harzuka makiyayan da manoma wanda ya juye zuwa rikici tsakaninsu.
Ministan shari’ar wanda ke tabbatar da kisan mutane 27 a rikicin wanda ya alakanta da kama karyar shugabannin gargajiya yayin taron masu ruwa da tsaki a Abeche ya yi fatar daukar matakan dakile rikicin.n
Daruruwan mutane ne suka fito zanga zangar adawa da gwamnatin mulkin sojin Chadi a jiya Asabar a babban birnin kasar N’Djamena, a yayin da ake ci gaba da zaman tankiya a kasar, biyo bayan mutuwar Idriss Deby Itno.
An samu tashin hankali a kasara watan Agustan nan , bayan da kungiyoyin fararen hula suka yi kira da a fito gangamin mnuna kyama ga gwamnatin sojin kasar, karkashin dan marigayi Idriss Deby, Mahamat Idriss Deby Itno, mai shekaru 37.
Masu zanga zangar sun caccaki Faransa, wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka, suna mai zarginta da goya wa sojoji baya su mulki kasar.
Idriss Debby ya mutu ne yana da shekaru 68, bayan da ya shafe fiye da shekaru 30 yana mulkin kasar.
Ya kwace mulki ne da karfin bakin bindiga a shekarar 1990.