A ranar talata ne aka tabbatar da Richado Sa Pinto a matayin sabon mai horas da ‘yan sananniyar kungiyar kwallonn kafa ta Esteghlal mallakin jamhuriyar musulunci ta Iran.
Richado Sa Pinto shine ya gaji Farhad Majidi wanda ya bar kungiyar bayan ya kaita ga matsayin daukan kofin Iran.
Sabon kocin na Esteghlal dan shekara 49 ya fara horaswa ne a kungiyar kwallo kafa ta Sporting CP a shekarar 2012 sa’annan ya horas da kungiyar kwallon kafa ta Braga, sa’annan Legia Warsaw, Vasco da Gama, Gaziantep da kuma Moreirense.
Richado ya sanya hannu a kwantaragin horaswa na shekara daya tare da damar tsawaita wa’adi bayan karewar wa’adin da ala cimma yanzu.
Kafin nan Esteghlal ta tattauna da Alex Nouri, Jose Morais, Reza Enayati da kuma Javad Nekounam.
A safiyar laraba 22 ga watan yuli ne dai sabon kocin na Esteghlal ya samu shiga jamhuriyar musulunci ta Iran domin fara gudanar da ayyukan horas da ‘yan wasan na Esteghlal.
Kungiyar Esteghlal dai na daya daga cikin kungiyoyin wasan kwallon kafa mafiya farin jini a yankin asiya.
A rade radi da ake yadawa cewa zuwa shekara mai zuwa kamfanin jirage na Qtar Air mallakin kasar Qatar zai zama mai daukar nauyin kungiyar kwallon kafan ta Esteghlal.
Kafafen yada labarin cikin gida na jamhuriyar musulunci ta Iran dai sun bayyan yadda aka tarbi sabon kocin a filin tashi da saukan jirage na Imam Khumaini dake babban hirnin Tehran a ranar labara 22 ga watan yuli.
Sai dai masana harkokin wasanni na kallon wannan lamari a matsayin abban cigaba ga kungiyar ta Esteghlal musamman duba da gogewar sabon kocin mai shekaru 49.
Iran dai na cikin na gaba gaba a harkokin wasanni a nahiyar Asiya inda taci kofuna a wasanni daba daban a matakin nahiyar asiya dama duniya baki daya.
Sa’annan Iran na cikin manyan kasashen Asiya wadanda ke dauko ‘yan wasa ko masu horaswa daga kasashen duniya.