Wakilan jam’iyyar Republican da dama na Amurka sun gabatar da wasu ƙudirori biyu da za su tura daliban da aka kama a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu zuwa Gaza na tsawon watanni shida tare da soke bizar ɗaliban ƙasashen duniya.
Kudirin farko, wanda aka yi wa laƙabi da “Antisemitism Community Service Act,” ya ba da shawarar aika duk wani “wanda aka yanke masa hukunci ko kuma aka tuhume shi da aikata ba bisa ƙa’ida ba” a harabar kwalejin Amurka tun daga Oktoba 7, 2023, don “zuwa yi wa al’umma hidima a Gaza” na aƙalla watanni shida.
Duk da yake ƙudurin bai ambaci sansanonin da aka kafa na goyon bayan Falasdinawa na musamman da suka yadu a jami’o’in Amurka ba, ya shafi harabar jami’o’in ne bayan ranar 7 ga Oktoba, 2023, ranar da Hamas ta kai harin ba-zata kan Isra’ila.
Wakilin Tennessee Andy Ogles ne ya gabatar da wannan doka mai cike da cece-kuce, wanda aka sani da matsayinsa na adawa da Falasdinu.
A watan Fabrairu, an yi rikodin dan majalisar yana cewa, “ya kamata mu kashe ‘su duka” don amsa tambaya game da mutuwar yaran Falasdinawa a Gaza.
Kididdigar doka ta biyu, mai taken “Dokar Nazarin Ƙasashen Waje,” tana neman ” soke takardar biza rukunin F, J, ko M” na duk wani baƙon da aka “kama shi saboda tarzoma ko zanga-zangar ba bisa ƙa’ida ba,” ko kuma waɗanda “aka kama yayin kafa, shiga, ko kuma” inganta sansanin zaman dirshan.”
DUBA NAN: Halin Da Dalibai Masu Zanga Zanga A Amurka Ke Ciki
Dan majalisa Jeff Duncan, wanda ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar tare da Randy Weber, ya bayyana goyon bayansa a wani rubutu a shafin X, yana mai cewa, “Ba ma bukatar masu goyon bayan Hamas a kasar Amurka suna karya dokokinmu da kuma tasiri ga matasanmu don ƙin Amurka da ‘yanci.”