Rahotanni sun ce, a kwanakin karshe na watan Safar sama da Maziyarta miliyan 6 186 ne aka hidimta masu a haramin Sayyid Imam Riza (AS) a wuraren shan shayi na Motahar Razawi.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, a cikin mafi daukakar ranaku na karbar bakuncin haramin Razawi mai alfarma baya ga bayar da hidimomi daban-daban an tarbi maziyarta miliyan shida da dubu 186 a wuraren shan shayi na Imam.
A kwanakin karshe na watan Safar, an bude wuraren shan shayi na Sayyidina Riza (a.s) a farfajiyar Ghadir, Kausar, Imam Hasan Mojtabi (a.s.) da lambunan Rezwan. Tun daga farkon kwanaki goma na ƙarshe na watan Safar waɗannan gidajen shan shayi suka fara maraba da maziyarta da maƙwabta sa’o’i 24 a rana ta hanyar cin gajiyar ƙarfin jerin gwanon jama’a da kuma bayarda sabis na ban mamaki ta mahangar ƙididdiga.
Gidajen shan shayin sun yi hidima ga ma’abota hidima na iyalan tsarki da tsarkakewa a lokutan hidima guda biyu tare da halartar turuwar masu hidima daga ko’ina cikin kasar.
Rahotanni sun ce, a kwanakin karshe na watan Safar, sama da maziyarta miliyan 6 da 186 ne aka hidimtawa tare da saukar baki na Imam Rida (AS) a wadannan wuraren shan shayi.
Tare da Sanarwa karshen watanni biyu na zaman makoki na bayin Allah / An daga koriyar tutar Razawi akan Kubbar haramin.
A kowace shekara da karshen watan Muharram da Safar na zaman makoki a hubbaren Razawi mai tsarki da kuma jera raneku uku na zaman shahadar Ali binu Musal-Riza (a.s.), inda a yayin wannan taro ya ke samun halartar masu hidina na wannan hubbare tare da gudanar da maye gurbin haramin Razawi mai tsarki da tutar kubba da suturar haramin Sayyidina Aliyul Riza (a.s.)
A cikin wannan taro da aka gudanar da safiyar yau a gaban maziyarta Imam na takwas (AS) ne wasu gungun ma’aikatan Hubbaren suka canza bakin lullubi da ke kan haramin da kuma tutar harami dake kan kubba, tare da maye gurbinta da koriyar tuta.
Source: ABNA