Jakadan kasar Iran a MDD Majid Takht Ravanchi ya bayyana cewa kekkyawar niyyar da manufofin siyasa masu kyau ne zasu samar da sakamako mai armashi a tattaunawar Vienna ta dagewa kasarsa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Rawanchi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabata a gaban kwamitin tsaro na MDD a birnin NewYork na kasar Amurka a jiya Talata.
IP ya kara da cewa jakadan yana magana ne a lokacinda kwamitin yake magana dangane da dabbaka kudurin MDD mai lamba 2231 wanda yak e goyon bayan yarjejeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran tsakaninta da manya-manyan kasashen duniya a shekara ta 2015.
A karshen watan da ya gabata ne aka farfado da tattaunawa don dagewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dora mata, da kuma sake raya jarjejeniyar ta JCPOA.
Gwamnatin kasar Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar a shekara ta 2018, sannan ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.