Rashin Tabukawar Kwamitin Tsaro Na Karawa Isra’ila Karfin Guiwar Ci Gaba Da Zaluntar Falasdinawa.
Mataimakiyar wakilin kasar Iran na dindin din a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya Zahra Ershadi ta fadi cewa rashin daukar mataki da kwamitin tsaron yake yi kan laifukan yaki da Isra’ila ke tafkawa kan Al’ummar Falasdinu da ma sauran kasashen yankin na kara mata karfin guiwa ci gaba da nuna mummar dabi’ar.
Ershadi ta yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da dauki matakin gaggawa na dakatar da Isra’ila daga ci gaba da take hakkin bil adama da dokokin kasa da kasa da ta ke yi
Har ila yau ta fadi cewa rahin tabuka komai daga bangaren kwamtin tsaro ya karawa isra’ila karfin guiwa ta ci gaba da tafka laifukan yaki kan alummar falasdinu da ake zalunta, da kuma keta hurumin kasashen daban daban a yankin, kuma rashin daukar mataki na shari’a da hukumta ta sun taimaka wajen bata kariya .
Idan ana iya tunawa a jiya ne sojojin Isra’ila suka yi amfani da motar ruguza gine- gine wajen rusa gidajen wasu falasdinawa da ake tsare da su wato yusuf Aasi da kuma Yehya Miri wadanda Isra’ila ke zargi da kashe wasu yahudawa a watan Aprilun da ya gabata.