Fadar mulkin rasha ta kremlin ta bayyana matsayar ta dangane da amfani da makamin nukiliya inda ta bayyana cewa, zzatayi amfani da makamin nukiliya ne kawai idan kasashen yammacin turai suka tsaurara takurawar da suke mata a yakin ta da kasar Ukraine.
Mai magana da yawun fadar mulkin rasha ta kremlin Dmitri Peskov ya bayyana cewa yakin dake gudana tsakanin rasha da ukraine bazai taba iya zama dalilin da za’a yi amfani da makamin nukiliya ba.
A wanna tattaunawa da kafar sadarwa da PBS Peskov ya bayyana cewa ”muna da tsarin mu wanda ya bayyana cewa babu lokacin da zamuyi amfani da makamin nukiliya sai idan mun lura cewa a kwai wata matsala wacce take barazana ga kasasncewar kasar mu, a wannan lokacin zamuyi amfani da makamin nukiliya domin kawar da kowacce irin barazana da take kokarin kawo karshen wanzuwar kasar mu”.
Peskov yace wanna matsaya ta rasha shine yasa kasashen yammacin turai ke tuhumar kasar sa da kokarin amfani da makamin nukiliya, inda ya bayyana hakan matsayin zancen wofi domin dama kowa yasan a kwai barazanar amfani da makamin nukiliya a duniya amma kowa ba son yaki yake ba sai dai idan barazanar rugujewar kasa ta bayyana sai amfanin da makamin nukiliya ya zama dole.
A watan daya gabata e dai shugaban kasar rasha Vladimir Putin ya umarci bangaren nukiliya na kasar sa dasu zama cikin shirin kota kwana.
Kasar rasha dai ta mallaki fiye da rumbunan nuikiliya 6000 wanda aka tabbatar sun fi wanda amurka ta mallaka.
Kasashen yammacin turai dai sun kakaba sabbin takunkuman tattalin arziki kan rasha bisa dogaro da yakin da rashan ta kaddamar a kan ukraine wanda suka shiga wata na biyu da kakaba takunkuman.
Kasashen na yammacin turai dai sun zargi rashan da aikata laifukan da suka sabawa dokokin kasa da kasa a yakin nata da ukraine inda ita kuma rashan take kokarin kare kanta gami da bayyana halaccin yakin nata a kan ukraine.