Rasha ta yi watsi da kiraye-kirayen ƙasashen duniya kan biyan diyya.
Ƙasar Rasha ta yi watsi da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi mata na biyan diyya kan ɓarnar da ta yi wa Ukraine.
Hakan na zuwa ne bayan da babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri’ar cewa dole Rasha ta fuskanci hukunci game da yaƙin Ukraine ciki har da biyan diyya ga abubuwa da ta lalata.
Shawarwarin da ake cimmawa a babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na da ƙima, to amma zauren ba ya da ƙarfin tursasa ƙasashe su yi aiki da su.
Rasha ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta dakatar da ƙasashen yamma daga yuƙurin amfani da kuɗaɗenta da ke ajiye asusunta na ƙetare domin biyan diyyar.
Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya zargi ƙasashen na Turai da ƙoƙarin ‘halasta sata’ da kuma karya dokokin duniya kan mallakar kadarori.