Rasha ta yi iƙirarin harbe jiragen Ukraine biyar.
Ma’aikatar Tsaro ta Rasha ta faɗa a yau Asabar cewa ta kai wa wata tashar sojojin sama ta Ukraine hari a Vasylkiv da kuma wata cibiyar sadarwa da ke Brovary da makamai masu linzami.
Dukkan wuraren na kusa da Kyiv babban birnin Ukraine, kamar yadda kamfanin labarai na Rasha Tass ya ruwaito.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da faruwar hakan ba ko kuma tasirin da harin ya yi.
“Da safiyar 12 ga watan Maris, an kai wani hari da makamai masu linzami masu dogon zango kan kayayyakin soja a Ukraine,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar mai suna Igor Konashenkov yayin taron manema labarai a Moscow.
“An lalata tashar sojan sama ta Vasylkiv da kuma tashar sadarwa ta sojojin Ukraine da ke Brovary.”
Ya ƙara da cewa makaman tsaron sama na Rashar sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine biyar.
READ MORE : Dalibi ya chakawa dan uwansa wuka a makarata har lahira.