Rasha Ta Yi Gargadi Akan Yiyuwar Batakashi Da Kungiyar Tsaro Ta “ Nato” A Yankin “ Artic’.
Jakadan Kasar Rasha a majalsiar yankin Artic, ko dungun duniya na Arewa, Nikolay Korchunov, ya yi ishara da ewa; Kasarsa ta damu akan yadda Amurka da kawayenta su ke kara karakaina a cikin yankin wanda zai iya jawo mummunan sakamamo na tsaro da kuma na muhalli.
Kamfanin dillancin labarun TASS na Rasha da ya ambato jakadan yana fadin cewa; Shigar da wasu kasashen da ba su cikin yankin na Artic, kuma mambobin kungiyar tsaro ta Nato, yana kara jawo damuwa. Kuma yana kara haifar da zaman zullumi akan yiyuwar samun matsaloli na tsaro da tsarin muhalli na yankin.”
A bayan nan dai Amurka ta kara yawan kai da komowar da take yi a yankin, inda ta shirya atisayen soja, da hakan ya sa jadakan na Rasha ya fadi cewa; “ Atisayen sojan da aka yi a bayan nan a arewacin kasar Norway,ba zai taimakawa zaman lafiyar da ake da shi a yankin ba.
Atisayen ya kunshi sojoji 15,000 da suka hada sojojin Amurka da na wasu kasashen kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.