Rasha Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Biden Dangane Da Putin.
Fadar Kremlin ta mayar da martani ga shugaban Amurka saboda kiran da ya yi na neman sauyin shugabanci a Rasha, bayan da Joe Biden ya ce takwaransa na Rasha ba zai iya ci gaba da mulki ba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin Kremlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Asabar, inda ya ce: “Biden baya da hurumin gaya Rashawa wanda zai shugabance su.
Biden dai ya zafafa kalamansa a kan takwaransa na Rasha Vladimir Putin, tun a ranar 24 ga watan Fabrairu, lokacin da shugaban kasar Rasha ya ba da sanarwar fara kaddamar da “ayyukan soji na musamman” da nufin kawo karshe abin da Rasha ta kira kokarin murkushe Rashawan Ukraine da gwamnatin kasar ke yi a yankunansu Donetsk da Lugansk da ke a gabashin Ukraine.
A cikin 2014, yankunan biyu sun ayyana kansu a matsayin sabbin jamhuriyoyi masu kwarya-kwaryan cin gashin kai, tare da kin amincewa da gwamnatin Ukraine da ke samun goyon bayan kasashen Yammacin turai.
Putin ya ce an kaddamar da ayyukan sojin ne domin “kare mutanen da suka shafe shekaru takwas suna fuskantar zalunci da kisan kare dangi daga gwamnatin Ukraine.”
Tun da farko a wannan rana, Biden ya ce a cikin wani jawabi mai zafi yayin zaman taron Poland cewa “wannan mutumin (Putin) ba zai iya ci gaba da zama a kan karagar mulki ba,” yana mai yin tir da aikin soja.
Ko a makon da ya gabata, Kremlin ta caccaki Biden saboda “cin mutuncin shugaba Putin, bayan da ya kira shi da “mai laifin yaki,” inda bayanin fadar ya ce Biden ya wuce gona da iri, kuma kalamansa za su iya kaiwa ga rusa alaka tsakanin baki daya tsakanin Amurka da Rasha.