Rasha Ta Kuduri Aniyar Kara Fadada Alakarta Da Koriya Ta Arewa A Dukkanin Bangarori.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kuduri aniyar fadada alakar da ke tsakanin kasashen rasha da kuma Koriya ta Arewa a dukkanin bangarori.
Kamfanin dillancin labaran KCNA na koriya ta arewa ya habarta cewa, Putin ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un a bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar Japan.
Rahoton ya kara da cewa, kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, za ta taimaka wajen karfafa tsaro da zaman lafiyar yankin Koriya da kuma Arewa maso Gabashin Asiya baki daya.
Shi ma a nasa bangaren Kim ya aike da wasika ga Putin inda ya ce an kulla kawance tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa a yakin duniya na biyu tare da samun nasara kan Japan, wanda haka lamari ne na tarihi wanda zai ci gaba da dawwamar da alaka tsakanin Rasha da Koriya ta arewa.
Kim ya ce, “Hadin kai da yin aiki tare tsakanin Rasha da Koriya ta arewa a dukkanin bangarori, shi ne zai rusa makircin makiya da suke barazana ga zaman lafiyar kasashen biyu, da ma yankin Asia da sauran yankuna na duniya, musamman a kasashe masu ‘yancin siyasa.
Wasikar dai ba ta fayyace makiyan da Kim ke nufi ba, amma gaba daya dai Pyongyang na amfani da Kalmar makiya wajen bayyana Amurka da kawayenta.
A watan da ya gabata, Koriya ta Arewa ta amince da Donetsk (DPR) da Jamhuriyar Luhansk (LPR), yankuna biyu na gabashin Ukraine a matsayin yankuna masu cin gashin kansu, kusan watanni biyar bayan da Rasha ta fara aikin soji na musamman a cikin Ukraine daya daga cikin yankunan tsohuwar tarayyar Soviet, inda ita Ukraine ta mayar da martani, ta hanyar yanke huldar ta da Koriya ta Arewa.