Dakarun tsaron Rasha na kara zafafa kokarin kame Severodonetsk, birni na karshe da ke da sojin Ukraine ke da karfi a yankin Luhansk.
Yayin da Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce kasarsa a shirye take ta yi musanya sojojinta da suka mika wuya a masana’antar karafa ta Azovstal da ke Mariupol da fursunonin Rasha dake hannunta.
Wani mai shiga tsakani na Rasha ya ce Moscow za ta yi la’akari kan musayar fursunoni wata kila don burin ceto Viktor Medvedchuk, hamshakin attajiri dan kasuwan Ukraine dake kusa da Shugaba Vladimir Putin, sai dai bai fayyace adadin fursunonin da za’a yi musayar ba.
Katafaren kamfanin makamashi na kasar Rasha Gazprom ya ce ya dakatar da shigar da iskar gas ga kasar Finland saboda kin biyan sa da kudin rubulles na Rasha.
A wani labarin na daban a kalla mutane hudu aka tabbatar da mutuwar su yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan da wani bene mai hawa uku ya yuguje a birnin Lagos dake Kudanci Najeriya.
Rahotanni na cewa benin mai hawa uku da ba’a karasa ginawa ba ya rikoto ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin a ranar Asabar.
Jami’an yace asalin ginin bungalow ne, amma ake kokarin mai da shi hawa uku.
Jihar Legas dai ta yi kaurin suna wajen rugujewar gine-gine a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da jikkatar mutane da dama.
Na baya-bayan nan shine wanda wani bene mai hawa uku ya ruguje a Ebute Metta,ranar 1 ga watan Mayun, inda mutane akalla 10 suka mutu.