Rasha Ta Kammala Kwace Iko Da Daukacin Lardin Lugansk A Ukraine.
Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya sanar da shugaban kasar Vladimir Putin kammala kwace da daukacin lardin Lugansk na kasar Ukraine.
A ranar jiya Lahadi 3 ga Yuli, 2022, Ministan Tsaro na Tarayyar Rasha Sergei Shoigu, ya sanar da babban kwamandan sojojin Tarayyar Rasha Vladimir Putin cewa, an kammala kwace iko da daukacin yankin Lugansk lardi mafi girma a cikin kasar Ukraine.
Ministan tsaron kasar ya bayyana cewa, sakamakon nasarar da sojojin kasar suka samu, wasu rukunin sojojin kasar Rasha, tare da hadin gwiwar rundunonin sojojin sa kai masu mara wa Rasha baya a Lugansk, sun kafa cikakken iko a birnin Lyschansk da wasu yankuna da ke makwabtaka da lardin.
READ MORE : Iran; Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Ci Gaba Da Tattaunawar Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Haka nan kuma Ministan tsaron na Rasha ya kara da cewa, sun kammala kwace wasu birane na daban a jiya, da suka hada da Belogorovka, Novodrogsk, Maloryazantsevo da Belaya Gora.
READ MORE : Jeff Bezos Mamallakin Amazon Ya Caccaki Biden Kan Matsalar Hauhawar Farashin Kayayyaki.
READ MORE : Za a maido da dangantaka tsakanin Poland da gwamnatin Sahayoniya.