Rasha Ta Kakabawa Wasu Jami’an Birtaniya Takunkumi.
A wani mataki na mayar da martani kasar Rasha a sanar da kakaba takunkumi kan wasu manayan jamian gwamnatin kasar Birtaniya guda 13 ciki har da fira ministan kasar Boris Johnson da ministan harkokin wajen Liz Truss da kuma na Tsaro wato Ben Wallace.
Idan ana iya tunawa a safiyar ranar 24 ga watan Fabareru ne shugaban kasar rasha Viladmir Putin ya sanar da fara kaddamar da kai hare-haren soja a yankin Donbas dake gabashin kasar Ukranin , da suka hada da Luhanks da Donetsk domin goyon bayan yan rasha da ke yankunan wanan yasa kasar Amurka da kawayenta na tarayyar Turai suka kakaba mata takunkumi.
A matakin ma mayar da martani ita ma kasa rasha ta haramtawa manayan jami’an gwamnatin da yan siyasar birtaniya shiga kasar Rasha, saboda matakin ba zata da kasar ta dauka musamman na sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an gwamnatin Rasha,
READ MORE : Alummar Moroko Sun Yi Zanga-zangar Goyon Bayan Masallacin Quds.
Rasha ta zargin birntaniya da kara ruruta wutar rikicin Ukrain ta hanyar aikewa da muggan makamai da kuma hada guiwa da kungiyar tsaro ta Nato, matakin na Birtaniya ya tunzura sauran kawayenta na turai wajen maka takunkumi kan Rasha.