Rasha Ta Jaddada Bukatar A Sauya Cibiyar MDD Daga Birnin NewYork Zuwa Wani Wuri.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta jaddada bukatar a dauke cibiyar MDD daga Amurka zuwa wata kasa.
Kamfanin dillancin labarab Mehr na kasar Iran ya nakalto Alexey Drobinin darakta mai kula da al-amuran tsare-tsare na ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha yana fadar haka.
Drobinin ya kara da cewa a lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta amince da dauki bakwancin dukkan kasashen duniya a cibiyar MDD da za’a gina a birnin NewYork a shekara 1945 ta dauki alkwarin ba zata yi amfani da wannan matsayin don tozartawa wasu kasashen duniya ba.
Jami’in Diblomasinyan ya kara da cewa a halin yanzu ba jami’an diblomasiyyar kasar Rasha kadai suke fuskantar walakanci da kuma jinkiri wajen samun visa don isa cibiyar MDD dake birnin NewYork ba, sai dai akwaiwasu kasashen duniya da dama wadanda Amurka take hana jami’an diblomasiyyarsu shiga Amurka don isa cibiyar MDD ba.
READ MORE : Najeriya Zata Biya Miliyon $496 Ga Wani Kamfanin Kasar Indiya Dangane Da Kamfanin Karafa Ta Ajaokuta.
Jami’in ya kara da cewa kafin a amince a maida cibiyar MDD daga Geneva zuwa NewYork a shekara 1951 Amurka ce take daukae nauyin kasha 25% na bukatun majalisar, don haka ne aka amince da maida cibiyar majalisar zuwa birnin NewYork.