Katafaren kamfanin makamashi na Gazprom na Rasha ya dakatar da isar da iskar gas zuwa Jamus, wanda shi ne na baya bayan nan da aka dakatar, abin da ya haifar da matsalar makamashi ga nahiyar Turai.
Gazprom ya kuma ce zai dakatar da samar da iskar gas ga babban kamfanin samar da iskar gas na Faransa Engie daga ranar alhamis bayan da ya gaza biyan basukan da ake bin sa a watan Yuli.
Tsagaitawar ta baya-bayan nan ta zo ne a daidai lokacin da kasashen Turai ke fuskantar hauhawar farashin makamashi tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a karshen watan Fabrairu, sannan ta dakile hanyoyin aika musu da iskar gas zuwa yankin.
Jamus wacce ta dogara da iskar gas daga Rasha, ta zargi kasar da amfani da makamashi a matsayin daukar fansa ga kasashen yamma.
Kungiyar Tarayyar Turai na shirin daukar matakin gaggawa domin yin garambawul ga kasuwar lantarki, domin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, inda ministocin makamashi za su yi wata tattaunawa ta musamman a mako mai zuwa.
A wani labarin na daban kuma Iran ta gabatar da ra’ayoyi kan martanin Amurka ga daftarin rubutu na EU kan farfado da yarjejeniyar 2015
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kan’ani ya ce Tehran ta ba da ra’ayinta kan martanin da Amurka ta mayar kan wani daftarin rubutu na EU na farfado da yarjejeniyar nukiliyar ta 2015.
“Bayan samun martanin da Amurka ta bayar, tawagar kwararrun Jamhuriyar Musulunci ta yi nazari sosai kuma an tattara martanin Iran tare da mikawa kodinetan martanin a daren yau,” in ji Kan’ani a safiyar Juma’a.
Jami’in ya kara da cewa an shirya martanin Iran “bayan kimantawa a matakai daban-daban.”
Source: ABNAHAUSA