Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa ba za ta sake bude bututun iskar gas mai suna Nord Stream 1 zuwa kasashen Turai ba sai sun dauke mata takunkuman tattalin arzikin da suka dora mata bayan ta shiga yaki a Ukraine.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov, yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki wadanda kungiyar Tarayyar Turau (EU) da Burtaniya da kuma Canada suka dorawa kasar da kuma wasu kamfanonin kasar ne suka sa Rasha ta dakatar da tura iskara gasa cewa kasar Jamus daga St. Petersburg zuwa arewacin kasar Jamus. Kuma matukar ba a cira takunkuman nan ba Rasa ba za ra sake turawa kasashen na Iskar gas ba.
Kakakin fadar Krimlin ta rasha ya kammala da cewa takunkuman da kasashen yamma suka dorawa kasar Rasha sun hana ta hatta kula da bututun man da ke kaiwa kasashen iskar gas, don haka kada su zargi kowa su zargi kansu.
A halin yanzu dai kasashen turai sun fara neman inda zasu sami isakar gas don dumama gidajensu da kuma aikin kamfanoninsu daga wasu kasashen duniya. For its part, Moscow began to significantly reduce its gas deliveries to Europe through the Nord
A wani labarin na daban mai bawa babban kwamandan sojojin kasar Iran shawara kan al-amuran tsaro ya bayyana cewa shirin makamai masu linzami na Jamhhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) ba abin tattaunawa a kai bane.
Majiyar muryar JMI ta nakalto Amir Khatami yana fadar haka, ya kuma kara da cewa tsarin harkokin tsaro na JMI ya ginu ne kan nuna karfi da tsoratar da makiya JMI ne, don haka babu wani abu da zai sa Iran ta amince da tattauna tsarin tsaron kasar ta wata kasa a duniya.
Khatami ya kara da cewa makiya JMI sun fito da ra’ayin tattauna tsarin makamai masu linzami na JMI bayan da suka ga irin ci gaba mai yawa wanda sojojin Iran suka samu a wannan bangaren.
Ya kuma jaddada cewa JMI zata ci gaba da inganta makamanta a dukkan matakan sojojin kasar don tabbatar da cewa makiya sun sai yi tunani mai zurfi kafin su yi kokarin farwa kasar da yaki.
Source: LEGITHAUSA