Rasha Ta Bukaci Sojojin Ukrain A Severodonetsk Su Ajiya Makamansu Su Mika Kai.
Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa ta bukaci sojojin Ukrain da suke samun mafaka a wani kamfani a birnin Severodonetsk na gabacin kasar da su ajiye makamansu kafin safiyar yau Laraba, don sojojin Rasha sun son kakabe hannun gwamnatin Ukrain daga iko da birnin, wanda yake cikin yankin Dambass na gabacin kasar da ya balle.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban cibiyar tsaron kasar Rasha, Mikhail Mizintsev, yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa ya bawa sojojin Ukraine da suke turjiya a birnin su ajiye makamnasu su mika kai zuwa karfe 6 na safe agogon kasar. In bah aka ba Rasha zata yi amfani da karfin don kammala aikin kwace birnin.
READ MORE : Habasha; Firai Ministan Kasar Ya Ce A Shirye Yake Ya Fara Tattaunawan Da ‘Yan Tawayen Tigray.
Kafin haka gwamnatin Lardin Luhansk ya bayyana cewa kasha 80% na birnin ya fada karkashin ikon sojojojin Rasha. Ya kuma kara da cewa sojojin Rasha tun kori sojojin Ukrain zuwa kamfanonon da suke bayan garin, inda akwai wasu farare hula kimani 500 da suke garkuwa da kamfanonin daga hare-haren sojojin Rasha.