Ofishin jakadancin Rasha da ke Tel Aviv ya sanar da cewa, bayan cimma yarjejeniya da karamar hukumar Kudus da aka mamaye, ta yanke shawarar bude ofishin jakadanci a wannan birni.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, A wani bangare na bayanin ofishin jakadancin kasar Rasha ta bayyana cewa: Kafa wannan ofishin jakadanci yazo ne Saboda mallakar wani fili ne a yankin inda ta yanke shawarar bude ofishin jakadanci a wannan birni da kuma cikakken aikin karfafa dangantakar abokantaka a tsakanin Rasha da Isra’ila, haka nan kuma ba ya cin karo da manufofin Rasha da ba sa canjawa na warware batutuwa cikin adalci na tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kazalika majiyoyin yahudawan sahyoniya sun tabbatar da wannan labari tare da sanar da cewa ofishin jakadancin Moscow dake birnin Tel Aviv ya sanya hannu kan wata yarjejeniya a kan haka a ranar 18 ga watan Mayu tare da taimakon ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin sahyoniyawan.