Jami’an tsaron Rasha sun kama ‘yan kasar fiye da dari 3 saboda gudanar da zanga-zangar kin jinin yakin da gwamnatin shugaba Vladimir Putin ya kadamar kan Ukraine a ranar Alhamis ta makon jiya.
A baya bayan nan hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar Rasha ta haramtawa kafafen yada labarai masu zaman kansu kwatanta harin da Moscow ta kai kan Ukraine a matsayin “mamaya” ko kuma shelanta yaki”.
Yayin da sojojin Rasha suka shiga birnin Kyiv na Ukraine, ma’aikatar tsaron Moscow ta umarci kafafen yada labaran Rasha su tsaya kan bayar da alkaluman da suka faru a hukumance.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta zargi wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu da yada bayanan da ba su da tabbas a cikin al’umma game da hare-haren da sojojin Rasha suka yi a garuruwan Ukraine da kuma kashe fararen hula.
A wani labarin na daban Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine zai dauki dogon lokaci sakamakon yadda al’amura ke tafiya.
Yayin da ya ke tsokaci akan halin da ake ciki a Ukraine, Macron ya ce yakin zai dauki dogon lokaci kafin aga bayan sa, saboda haka ya dace duniya ta shirya fuskantar matsalolin da yakin zai haifar.
Macron ya shaidawa taron bikin nuna amfanin gona cewar ya dace jama’ar kasar su shirya tinkarar matsalar da zata biyo baya.
Shugaban na Faransa ya katse halartar bikin baje-kolin amfanin gonar wajen komawa fadarsa domin tinkarar rikicin dake gudana a Ukraine.
Macron ya ce yaki ya koma nahiyar Turai, kuma shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya haifar da shi akan mutanen Ukraine wadanda da ke bijirewa kasar sa da kuma rungumar kasashen Turai.
Shugaban ya sake kiran wani taron majalisar ministocin sa da na tsaro na gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a Ukraine.
Takunkumin da aka kakabawa Rasha sakamakon wannan yakin zai yi matukar illa ga bangaren cinikin barasar da Faransa ke sarrafawa, yayin da shugaba Macron ke Nazari akan yadda za’a taimakawa bangaren.
Shugaba Macron ya taka rawa sosai wajen hana barkewar yakin ta hanyar diflomasiya, inda ya dinga kai gwauro yana kai mari tsakanin shugabannin Rasha da Ukraine da Jamus da kuma Amurka domin ganin an kaucewa tashin hankalin.