Manyan kasashen yammacin duniya na gaggawar mayar da martani ga matakin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya dauka na amincewa da ‘yancin cin gashin kan wasu yankuna biyu na ‘yan tawaye dake gabashin Ukraine da kuma tura sojoji yankin, yayin da Amurka da kasashen Turai ke shirin sanya mata takunkumai.
Amurka
Fadar White House ta yi maraba da matakin da Jamus ta dauka kan bututun mai, ta kuma ce za ta bayyana nata matakan nan bada dadewa ba, yayin da Birtaniya ta sanya takunkumi kan bankunan kasar Rasha biyar da kuma wasu attajiranta uku.
Ukraine
A halin da ake ciki, Ukraine, ta kira babban jami’in diflomasiyyarta daga rasha, a daidai lokacin da shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya yi gargadin cewa matakin Putin na amincewa da yankunan da suka balle, tamakar shirin mamayar soji ne ya fito karara.
Estonia
Shugaban kasar Estonia Alar Karis wanda yayi gaggawar zuwa Ukraine domin jajinta masa, yayi Allah wadai da matakin Rasha.
Faransa
Firaministan Faransa Jean Castex yace Rasha na keta dokokin kasa da kasa, yana mai cewa kasar za ta goyi bayan duk wani takunkumin da za’a kakabawa Rasha yayin da kuma za ta ci gaba da neman sulhu.
A wani labarin na daban Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Rasha Vladimir Putin da na Ukraine Volodymyr Zelensky a wanna Lahadi a wani yunkuri na karshe da yake yi na dakile shirin Moscow na mamaye Ukraine.
Haka zalika tattauanawar ta yau na zuwa ne, kwana guda bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya shaidawa Macron cewa ba zai mayar da martani ga abin da ya kira tsokanar Rasha ba.