Rasha; Dole Ne Amurka Da Kungiyar Tsaro Ta NATO Su Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Ukrain.
Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kasar Amurka da kuma kungiyar tsaro ta NATO su daina aika makamai zuwa kasar Ukrain idan da gaske suna son zaman lafiya a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban karamar majalisar dokokin kasar Rasha Vyacheslav Volodin yana fadar haka a shafinta na Telegram a jiya Asabar.
Labarin ya kara da cewa idan wadannan kasashen suna son zaman lafiya a kasar Ukrain su dakatar da kwararar makamai zuwa kasar ta Ukraine, don Rash aba zata daina yaki ba, sai kasar Ukrain ta zama bata da makamai sannan ta bar ra’ayin NAZI.
READ MORE : Kasashen Habasha, Masar Da Sudan Suna Tattaunawa A Asirce A UAE.
Kafin haka dai ministocin tsaro na kasashen NATO sun gudanar da taron gaggawa a birnin Brussels inda suka tsaida shawarar tallafawa mutane Ukrai da makamai don kare kansu da aminda suka kira kasarsu daga mamayar Rasha.
Daga karshe Volodin, ya ce idan Amurak da sauran klasashen Turain suna son a dakatar da yaki a Ukrain su fara da kansu, wato su daina aika makamai zuwa kasar Ukrain, don yin haka yana hana tattaunawar da ake da kasar Ukrain ci gaba.