Rasha Da Ukraine Zasu Sake Tattauanwa Yau Litini.
Nan gaba a yau Litinin ne ake sa ran wakilan kasashen Rasha da Ukraine, za su sake tattaunawa ta kafar bidiyo, yayin da aka shiga kwana na 19 na matakin sojin da Rasha ta ce tana dauka kan Ukraine.
Da yake bayyana hakan a jiya Lahadi, kakakin fadar gwamnatin Rasha Dmitry Peskov, ya ce an dauki wannan mataki ne, saboda bukatar da ake da ita ta ci gaba da maida hankali kan muhimman batutuwa da dama.
Shi ma mashawarcin shugaban Ukraine Mykhailo Podoliak, ya tabbatar da hakan a sakon da ya wallafa a shafin sa na Tiwiwa.
READ MORE : IRGC, Ta Sanar Da Kai Jerin Hare hare Kan Cibiyoyin Leken Asirin Isra’ila A Erbil.
Tun daga ranar 28 ga watan Fabarairu, wakilan kasashen biyu suka fara tattaunawa kai tsaye a Belarus, inda suka gudanar da zama har sau 3, ko da yake ba su kai ga cimma wani sakamako na a zo a gani ba.
A halin da ake ciki dai bayanai sun ce dakarun Rasha na kokarin yi wa birnin Kiev kawanya, yayin da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sha alwashin jan daga.