Ranakun Fajr Ranar Da Imam Khomeini Ya Dawo Tehran
A Iran, an fara bukukuwan shekaru 43 na zagayowar ranakun nasara juyin juya halin musulinci a kasar.
A rana irin ta yau ce 1 ga watan Fabarairun 1979, Imam Khomeini wanda ya assasa jamhuriyar musulinci ta Iran, ya dawo birnin Tehran daga birnin Paris na faransa bayan gudun hijira na tsawon shekaru 15.
Dubun dubatar ‘yan Iran ne suka masa tarba a filin jirgin saman Mehrabad, bayan faduwar mulkin sarki Shah.
Bayan zuwansa ya wuce kai tsaye a makabartar Behesht-e Zahra, domin tuna wadanda suka yi shahada yayin gwagwarmayar juyin jyua halin inda kuma ya yi jawabinsa na farko.
A Iran dai ana amfani da ranakun goman farko na watan Fabarairu ana bukukuwa da taruruka iri daban daban domin murnar cin nasara juyin juya halin.
Saidai sakamakon cutar korona a bana ma za’a gudanar da bukukuwan cikin matakan yaki da annobar.
024