Isra’ila ba za ta iya tantance ko taswirar dukkan hanyoyin sadarwa na ramukan Hamas ba.
Domin domin samun nasara, dole ne ya zamo ta iya lalata akalla kashi biyu bisa uku na ramukan karkashin kasa na Hamas.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: a wani labarin da jaridar Foreign Policy ta fitar na cewa, gwamnatin yahudawan sahyoniya tana ci gaba da lalata manyan ramukan Hamas sannu a hankali kuma cikin wahala, ta bayyana hakan a matsayin mafi girman raunin da Isra’ila ta fuskanta a yakin da Hamas.
Wannan jaridar ta Amurka ta ba da rahoton cewa: Rugujewar da Isra’ila ke yi wa ginin karkashin kasa na kungiyar Hamas yana da wahala sosai.
A cewar wannan jarida ta Foreign Policy, ramukan kasa na Hamas, waɗanda ke da sarƙaƙƙiya sune hanyar ɓoye dakarun ƙungiyar da fursunoni, a zahiri wani muhimmin sashi ne na kayayyakin aikin soja na ƙungiyar. Tsarin da a cewar marubucin wannan labarin, shine babban rauni na Isra’ila a yakin da Hamas.
Marubucin ya ci gaba da gabatar da wadannan tambayoyi guda biyu: wane mataki Isra’ila ta kai na lalata hanyar sadarwa ta Hamas?
Kuma har yaushe za’a dauka kafin a shawo kan wannan barazanar gaba daya? Ya ambata: Yaƙe-yaƙe na rami sun kasance ɗaya daga cikin mafi muni kuma mafi rikitarwa nau’ikan yaƙe-yaƙe.
Alal misali, a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, an kashe dubban sojojin Biritaniya da suka lalata wuraren da Jamusawa ke karkashin kasa. Shekaru bayan haka, Amurka ta yi kokari sosai wajen fatattakar abokan gaba a cikin zurfin ramukan da aka gina a Vietnam, Afganistan da Iraki, kuma a yanzu Isra’ila ta san da hakan sosai.
Jaridar Foreign Policy ta kara da cewa: A saboda haka ne gwamnatin sahyoniyawan da ke da karfin soji mafi ci gaba wajen ganowa, tsara taswirori, kawar da ramuka da lalata su, ta shiga yakin da ake yi da Hamas a halin yanzu. To sai dai kuma hakan bai hana Hamas tono ramukan ba kai har ma da kara kalubalen yakin karkashin kasa ga Isra’ila da kuma haddasa hasarar da hatta kwararrun sojojin Isra’ila suka shiga wadannan ramukan bayan an jefa bama-bamai a cikinsu.
A wani bangare na wannan rahoto, dangane da yadda aka gina waɗannan ramukan: Tsarin farko na wannan rukunin a farkon shekarun 2000 ya dogara ne akan ƙarfafawa da allunan katako.
Amma hanyoyin sadarwa na yanzu sun fi zurfi kuma sun fi karfi, kuma Hamas ta yi amfani da fasahar zamani wajen gina su kuma ta sami damar inganta karfinta na karkashin kasa a cikin shekarun da suka gabata.
Don haka, dole ne sojojin Isra’ila su bi tsarin da ya dace don ci gaba a cikin wannan karkatacciyar hanya mai hatsarin gaske kuma su yi amfani da sulke motocin buldoza masu sulke don share kasa don gano kofofin ramin.
Waɗannan mashigar, waɗanda aka fi sani da ramukan Ƙarƙashin kasa haƙiƙa ɓoyayyu ne masu mutuƙar tsoratarwa, waɗanda suka bambanta girma da siffa kuma galibi ana shigar da tarkunan bam masu fashewa a cikinsu.
Wadannan ramukan na baiwa dakarun Hamas damar fitowa daga kasa suna harbin sojojin Isra’ila sannan su sake bacewa cikin dakikoki.
Dangane da wannan lamarin dai, wannan jaridar ta kara da cewa Isra’ila ba za ta iya tantance ko taswirar dukkanin hanyoyin kasa na Hamas ba.
Sabada domin samun nasara, dole ne ya zamo an lalata akalla kashi biyu bisa uku na ramukan karkashin kasa na Hamas.
A wani bangare na wannan rahoto, an ambaci yunkurin da Isra’ila ta yi na sakin ruwan teku a cikin ramuka; Bisa ga hujjar marubucin, wannan aikin zai iya yin tasiri ne kawai idan an yi amfani da ruwa mai girma da kuma matsa lamba don lalata tsarin ramin gaba daya.
Sai dai kuma kalubalen da Isra’ila ke fuskanta bayan aika ruwan teku shi ne nisantar wasu ramuka daga gabar tekun da kuma yiwuwar ajiye fursunoni a wurin, lamarin da ka iya hana yahudawan sahyuniya aiwatar da wannan yunkurin.
A ƙarshe, ya kamata mu sani cewa yayin da Isra’ila ke aiki kowace rana don lalata cibiyar sadarwar kasa ta Hamas, ana samun ƙarin ramuka a kowace rana. Batun da zai iya sa wannan aikin ya daɗe kafin kammalawa.
Source: LEADERSHIPHAUSA