Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Masu lura da al’amura dai na ganin ramukan karkashin kasa na Gaza na daya daga cikin dalilan da suka sa sojojin Isra’ila suka jinkirta kai hare-hare ta kasa kan Gaza. Ramukan da al’ummar Gaza ke amfani da su wajen isar da man fetir da magunguna da kuma domin kare gwagwarmaya daga hare-haren Isra’ila.
Kafar yada labaran Ingila ta Middle East Eye ta rawaito cewa “Isra’ila na shirin cike ramukan Hamas da iskar gas” domin kawar da wannan mummunan mafarki daa take jin tsoronsa.
A wani labarin na daban babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: Ya kamata masu Tabligi su san irin ladubba da jawabai da za su yi mu’amala da masu sauraro da shi; Game da wannan, ya kamata a horar da mai wa’azi yadda zai bayar da amsoshi ga tambayoyin da ake da shubuha akansu.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: tawagar jagororin majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya a kasar Iraki, wadanda suke sansanin horo a birnin Qum, sun gana da Ayatullah Reza Ramezani, Babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (a.s) kafin azahar din jiya – Laraba 3 ga watan Aban 1402.
Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya a wannan taro da yake maraba da baki, ya bayyana irin yadda Isar da addini yake da muhimmanci da cewa: A yau kula da hanyoyin isar da sakon addini daban-daban, da kayan aikin isarwa, da masu sauraron wa’azi na da matukar muhimmanci ci gaban duniya.
Yayin da yake jaddada zamanantar da masu wa’azin tabligi da hanyoyin wa’azi, ya ce: Aikin masu Tabligi ya yi nauyi a yau, kuma Majalisar Ahlul-baiti (A.S) na da kyakykyawan damar wa’azi a Iraki ta fuskar yawa da inganci.
Yayin da yake jawabi ga shugabannin Majalisar Ahlul-Baiti (AS) na kasar Iraki, ya ce: Wajibi ne a hada littafin da ke dauke da bayanan yadda ake tabligi ta yadda za a shigar da fasahar isar da sako a cikinsa.