Shahararren dan wasan Spain Sergio Ramos na iya buga wa PSG wasa a karon farko tun da ya koma kungiyar a wasan gasar zakarun nahiyar Turai na ranar Laraba, a fafatawa da Manchester City.
Ba mamaki Ramos ya kasance a benci a wasa tsakanin manyan kungiyoyin biyu, inda ake ganin Marquinhos da Presnel Kimpembe za su fra wasana matsayin masu tsaron baya, wato 5 da 6 kenan.
Ramos ya isa psg ne bayan da ya gwada bajintarsa a Madrid, inda ya lashe gasar kofin duniya da na nahiyar Turai 2, da kuma kofunan zakarun nahiyar Turai 4.
City ke kan gaba arukuninsu da maki 9, ta baiwa PSG tazarar maki 1.
A wani labarin na daban kungiyar Real Madrid ta sallami kaften dinta Sergio Ramos bayan ya shafe tsawon kakanni 16 yana taka mata tamola, yayin da ta ce, a gobe Alhamis za ta yi masa bikin karramawa kafin ban-kwana da shi baki daya.
Za a karrama gwarzon dan wasan a bikin da zai samu halartar shugaban Real Madrid, Florentino Perez.
Dan wasan mai shekaru 35, ya yi ta fama da rauni a wannan kaka kuma wasanni biyar kacal ya buga wa kungiyar tun farkon wannan shekara.
A jumulce Ramos ya buga wa Real Madrid wasanni 671 tare da jefa kwallaye 101 a kungiyar, inda kuma ya lashe mata kofunan La Liga biyar, da kofunan Gasar Zakarun Turai hudu da kuma Copa del Rey guda biyu.
Ramos da Real Madrid sun gaza cimma matsayar tsawaita masa kwantiraginsa wanda zai kawo karshe a ranar 30 ga wannan wat ana Yuni.