Ayatullah Ramezani, a yayin da ya ziyarci asibitin Iran da ke Nairobi, ya yaba da ayyukan jin kai da wannan asibitin ke yi.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, a cikin ziyarar da Ayatullah Ramezani ya kai nahiyar Afirka, babban sakataren majalisar duniya na Ahlul-baiti (AS) ya ziyarci asibitin kula da lafiya na kasar Iran da ke birnin Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Dr. Faqihi, wakilin Iran a wannan asibitin, ya kuma yi bayani game da hidima da ayyukan jinya a wannan asibitin.
Yayin da yake yabawa ayyukan jin kai na wannan asibitin, Ayatullah Ramezani ya ce: Kenya za ta iya zama cibiyar kula da lafiya a nahiyar Afirka.
Source: ABNA