Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Amurka Joe Biden, kwana guda bayan da kasar ta kauracewa kada kuri’a kan kudirin dakatar da kasar Rasha daga hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin da ta yi a Ukraine.
Sa’o’i kadan bayan haka, Afirka ta Kudu na daga cikin kasashe 58 da suka ki kada kuri’a kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya dakatar da Rasha daga kwamitin kare hakkin bil’adama na MDD a matsayin ladabtar da mamayar Ukraine.
Wannan dai shi ne karo na uku da Afirka ta Kudu ke kauracewa kada kuri’a kan kudurorin da aka amince da su kan yakin.
Ramaphosa ya wallafa a shafinsa na twitter a wannan Juma’a cewa ya tattauna da shugaba Biden ta wayar tarho, kuma sun amince da bukatar tsagaita bude wuta da tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha.”
A wani labarin na daban Shugaban majalisar dattawa Najeriya, Ahmad Lawan ya roki ‘yan Najeriya da su sake baiwa jam’iyyar APC mai mulki wata dama.
Shugaban majalisar dattijai ya kaddamar da ginin wata cibiya ta gyaran hali a asibitin masu tabin hankali na tarayya da ke Budo-Egba a karamar hukumar Asa, sannan ya kaddamar da cibiyar kula da lafiya ta Idi-Isin Community Heatlh Centre da ke Unguwar Okolowo a Ilorin, wanda Oloriegbe ya gina.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, wanda lawan ya gada, na daga cikin wadanda suka wakilci mazabar Oloriegbe a Majalisar.