Ramadan; Yadda Musulmai a Birtaniya suka yi azumi a cikin ƙunci.
Yayin da watan Azumin Ramadan ke zuwa karshe a wannan Lahadin, ƙungiyoyin agaji sun ce iyalai Musulmai da dama sun shiga cikin hali na ƙuncin rayuwa inda suke shan wahala wajen samun abincin da za su yi buɗa-baki.
Hauhawar farashin man fetur da makamashi da kuma kayan masarufi sun shafi mutane da dama a sassa daban-daban, inda hauhawar farashin kayayyaki ta kai kololuwa watau matakin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 30.
Kungiyar Agaji ta Trussell Trust ta raba abinci sama da miliyan biyu daga 2021 zuwa 2022 inda sama da 830,000 ya shiga hannun yara kanana.
Wannan Ramadan shi ne na farko a cikin shekaru biyu da Musulmai suka samu damar yin buɗa-baki tare da wasu – a yanzu an janye da dama daga cikin dokokin daƙile yaduwar annobar korona.
A lokacin azumin Ramadan, Musulmai suna cin abinci sau biyu a rana – sau ɗaya kafin ketowar alfjir, da kuma sau ɗaya idan rana ta faɗi.
A lokacin buɗa-baki ana son su ci abinci tare da ‘ƴan uwa, abokai da jama’ar unguwarsu.
Amma hauhawar farashin kayayyaki ta sa mutane da yawa suna rayuwa cikin kunci.
Arshi Begum da ke zama a East Ham, da ke gabashin Landan tare da mijinta da yaronsu dan wata shida, ta ce ta dogara ne a kan abincin da take samu daga kungiyoyin agaji irin su shinkafar basmati da garin fulawa da nama da madara da kuma famfas.
Ta shaida wa BBC cewa: “Ba don kungiyoyin agaji ba da ban samu abincin buda-baki ba, in ban da ruwan sha.
“Abincin da muke samu daga wurin kungiyoyin agaji na taimaka mana mu adana akalla £100 a kowane mako wanda muke amfani da shi domin biyan wasu bukatunmu masu muhimanci.”
Sai dai Arshi da mijinta sun tashi daga gidansu kuma a halin yanzu suna zaune ne a wani gida tare da wasu mutane.
Dukansu suna aiki, amma da zarar sun biya kuɗin haya da kuma na bukatunsu sun ce ba sa samun kuɗin abinci.
“Ramadan da ya gabata, muna zaune a gidanmu kuma muna cin abinci iri-iri a lokacin buda-baki,” amma yanzu . “Wannan mafarki ne kawai,” in ji ta.
Wasu kungiyoyin agaji sun shaida wa BBC cewa sun samu karuwa a yawan Musulmai da suka nemi taimako a azumin watan Ramadan.
Gidauniyar Zakka ta kasa, wadda ke raba zakka ga Musulmai mabukata a fadin kasar Birtaniya, ta ce ta samu bukatu 1,746 na neman agaji a cikin watan Ramadan, idan aka kwatanta da 1,053 a irin wannan lokaci a bara.
Ita ma kungiyar agaji ta Islamic Relief ta ce ita ma ta samu irin wannan bukata kuma an fi son nama da shinkafa da fulawa.
Rifhat Malik, daga kungiyar agaji ta ‘Give a Gift’ da ke Leeds , ta ce ba su ta ba samun mabukata kamar na watan azumin Ramadan na bana ba.
Ta ce “muna kula da cibiyoyi abinci guda hudu kuma mun rika raba abinci cikin kunshi leda sama da 200 a kowane mako a wannan Ramadan.”
Ta kara da cewa mabukata sun karu da kashi 30 idan aka kwatanta da bara.
Berlin Mirre da yaranta biyar masu shekara biyu zuwa 14 na cikin wadanda suke samun taimakon kungiyar Give a Gift ta Rifhat Malik.
Berlin ta ce tana wahala wajen biyan bukatunta na yau da kullum saboda a ko yaushe farashin kayayyaki na hauhauwa.
“Farashin komai ya tashi tun azumin watan Ramadan na bara. Gwamnati ba ta bani isasshen kuɗi da zan kula da kai na da kuma yarana su biyar.”
‘Shekara ce mai muhimanci ‘
Kakakin gwamnati ya shaida wa BBC cewa: “Mun fahimci cewa mutane na rayuwa cikin wahala saboda hauhawar farashin kayayyaki kuma wannan na janyo damuwa ga iyalai Musulmai musamman a wannan lokaci mai muhimmanci a shekara.
“Ko da yake ba za mu iya kare kowa daga kalubalen da duniya take fuskanta ba, mun ware fam biliyan 22 domin tallafawa iyalai karkashin tsarin kashe kudi na bana.”
Karamar ministar kula da mata ta jam’iyyar Labour, Anneliese Dodds ta ce: ” Abin takaici ne cewa iyalai Musulmai da dama sun shiga cikin matsi kuma ba sa ma iya samun abinci da za su yi buda-baki.
“Labour na kira da a samar da wani Shirin kasafin kudi cikin gaggawa domin rage radadin da iyalai Musulmi suke ji tare da ganin cewa kamfanoni mai da iskar sun rage harajin da iyalai suke biya zuwa fam 600”, in ji ta.