Ra’isi; Zaman America A Afghanistan Ya Lalata kasar.
Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran da yake ganawa da sabon jakadan kasar Latvia, Peteris Vaivars lokacin da ya mika takardar shedar kama aiki, ya bayyana cewa kasancewar sojojin America da kungiyar tsaro ta Nato a kasar Afghanistan bai haifar da komai ba banda lalata kasar da yiwa alummar kasar kasan kare dangi
Har ila yau bangarorin biyu sun tattaunawa game da dangantakar dake tsakaninsu, ya kara da cewa yanzu duniya tana fuskantar manyan matsaloli da kuma rashin Adalci da aka nunawa wasu kasashe kamar Afghanistan da Falasdinu, don haka iran tana adawa da duk wani abu da zai jefa duniya cikin yaki da rashin adalci
Da yake ishara game da rikicin Ukrain da rasha kuwa ya ce yana fatan rikicin ba zai kawar da hankalin duniya kan abin da ke faruwa a kasar Afghanistan ba, da sauran mutanen kasashen dake da mafi yawan yan gudun hijira.
Daga karshe ya.
jaddadawa sabon jakadan irin dangantakar dake tsakanin kasahen biyu da kuma.
kokarin da suke yi na kara bunkasa ta a bangarori daban- daban.
RAED MORE : Guteress Zai Ziyarci Rasha A Wannan Talata.
READ MORE : Sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi Bafalasdine a sansanin Aqabat Jabr da ke Jericho.